Allah Sarki Yadda Wata Mata Ta Kwada Mijinta Kalli Cikakken Bidiyon👇👇👇…
NISHAƊI:🥰 Wata mata ta gwada mijinta domin ta san irin tsananin son da yake mata, sai ta rubuta takarda tana mai cewa; “Na gaji da zama da kai kuma ba zan iya ci gaba da zama dai a matsayin mata da miji ba ko kaɗan”
Bayan ta rubuta haka sai ta ajiye takardar kan gado, ita kuma sai ta shige ƙarƙashin gadon tana jiran ta ga abunda zai faru idan ya zo ya ga saƙonta.
Da zuwansa ya lura da takardar ya ɗauka ya karanta, kawai sai ya ɗau biron ya juya takardar ya mayar mata da amsa, bayan haka sai ya fara waƙe-waƙe yana rawa, nan take ya ɗauko wayarsa ya kira lambar wata budurwa ta sa yana mata albishir cewar ta samu dama a wajensa, matarsa ta gudu da kanta, ko dama ya yi kuskuren auren matar ita ya kamata ya aura tun farko, dan haka yana tayata murna sai yazo.
Nan take ya canja kaya ya fita cikin murna da jin daɗi.
Bayan fitarsa hankalinta a tashe cikin hawaye matar tasa ta fito ƙarƙashin gadon ta ɗauki takardar domin ganin me ya rubuta mata shima.
Tana duba takardar sai ta ga ya rubuta; “Ina ganin ƙafarki a ƙarƙashin gado, kuma ba wacce na yi waya da ita, zan je ne na siyo biredi.”
“Ki dena wannan wasan naki na wauta, ki tashi ki shirya mana abunci”😜
Shin a ganinku wa ya fi ƙaunar wani a cikinsu?
Fatan Alkhairi 🙏.